Accra (lafazi : /akra/) Birni ne da ke a yankin Birnin Accra, a ƙasar Ghana. Shi ne babban birnin ƙasar Ghana sannan kuma da babban birnin yankin Birnin Accra. Accra tana da yawan jama'a 2,270,000, bisa ga jimillar 2012. An gina birnin Accra a karni na sha biyar bayan haifuwan annabi Isa.