Musulunci

Addinin Musulunci Shine Addinin gaskiya shine wanda ba a bautawa kowa sai Allah Kuma Annabi Muhammad (saw) manzon sa ne Kuma Shi dan sako ne na Allah (SWT).

Annabi Muhammad (saw), tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi,[1] shi ne manzo wanda Allah ya aiko shi zuwa ga mutane baki ɗaya kuma na karshen/cikamakin annabawa a duniya domin ya sake jaddada addinin Allah, a yi imani da Allah wanda ya halicci kowa da komai. Addinin musulunci na da mabiya a duk fadin duniya kuma mafiya yawa su na zaune ne a yankin gabas ta tsakiya da yankin Afrika ta Arewa wadanda mafi yawansu Larabawa ne masu bin addinin musulunci, sai dai akwai dunbin mabiya addinin musulunci a ko'ina a fadin duniya.[2] Ma'anar Addinin Musulunci shi ne yarda da mika wuya ga Kaɗaita Allah Maɗaukakin Sarki, wato shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma annabi Muhammad Manzonsa ne (Ma'aikinsa ne), bayan haka ka/ki yarda da dukkan abubuwan da ya umarci al'umarsa haka kuma da wadanda ya hana su, da mika wuya ga umarnin Allah Ubangijin talikai, tare da tsarkaka daga kafirci (sanya kishiya wa Allah) da kafirai"Allah Madaukakin Sarki shi ya aiko Manzonsa Annabi Muhammadu (tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi) da Al Kur'ani Mai Girma domin ya zamo shiriya da rahama ga halittu baki daya, an kuma bayyana musulunci a matsayin addinin dake da saurin karin yawa a duniya a kullum wanda ke da Adadin musulmai na Duniya sun kai kusan kashi 24.1% na dukkan mutanen Duniya, wato fiye da Musulmai Biliyan Daya da Miliyan dubu dari takwas (1,800,000,000) a fadin duniya.[3]

  1. https://dictionary.cambridge.org/pronunciation/english/islam
  2. https://www.britannica.com/topic/Islam
  3. https://www.dictionary.com/browse/islam

From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Nelliwinne