Najeriya

Najeriya
Nijeriya (ha)
Naigeria (ig)
Nàìjíríà (yo)
Tutar Najeriya Tambarin Najeriya
Tutar Najeriya Tambarin Najeriya


Take Tashi Ya Yan Kasa

Kirari «Unity and Faith, Peace and Progress»
«Единство и вяра, мир и прогрес»
«Good people, great nation»
«Undod a Ffydd, Heddwch a Chynnydd»
Official symbol (en) Fassara Costus spectabilis (en) Fassara
Suna saboda Nijar
Wuri
Map
 9°N 8°E / 9°N 8°E / 9; 8

Babban birni Abuja
Yawan mutane
Faɗi 211,400,708 (2021)
• Yawan mutane 228.85 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Bangare na Afirka ta Yamma
Yawan fili 923,768 km²
Wuri a ina ko kusa da wace teku Tekun Atalanta
Wuri mafi tsayi Chappal Waddi (2,419 m)
Wuri mafi ƙasa Lagos Island (−0.2 m)
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Taraiyar Najeriya
Ƙirƙira 1 Oktoba 1963
Tsarin Siyasa
Tsarin gwamnati Jamhuriyar Tarayya
Majalisar zartarwa Majalisun Najeriya
Gangar majalisa Majalisar Taraiyar Najeriya
• Shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu (29 Mayu 2023)
Majalisar shariar ƙoli Kotun Koli Ta Najeriya
Ikonomi
Nominal GDP (en) Fassara 440,833,583,992 $ (2021)
Kuɗi Naira
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Suna ta yanar gizo .ng (en) Fassara
Tsarin lamba ta kiran tarho +234
Lambar taimakon gaggawa *#06# da 199 (en) Fassara
Lambar ƙasa NG
Wasu abun

Yanar gizo nigeria.gov.ng
Najeriya
Nijeriya (ha)
Naigeria (ig)
Nàìjíríà (yo)
Tutar Najeriya Tambarin Najeriya
Tutar Najeriya Tambarin Najeriya


Take Tashi Ya Yan Kasa

Kirari «Unity and Faith, Peace and Progress»
«Единство и вяра, мир и прогрес»
«Good people, great nation»
«Undod a Ffydd, Heddwch a Chynnydd»
Official symbol (en) Fassara Costus spectabilis (en) Fassara
Suna saboda Nijar
Wuri
Map
 9°N 8°E / 9°N 8°E / 9; 8

Babban birni Abuja
Yawan mutane
Faɗi 211,400,708 (2021)
• Yawan mutane 228.85 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Bangare na Afirka ta Yamma
Yawan fili 923,768 km²
Wuri a ina ko kusa da wace teku Tekun Atalanta
Wuri mafi tsayi Chappal Waddi (2,419 m)
Wuri mafi ƙasa Lagos Island (−0.2 m)
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Taraiyar Najeriya
Ƙirƙira 1 Oktoba 1963
Tsarin Siyasa
Tsarin gwamnati Jamhuriyar Tarayya
Majalisar zartarwa Majalisun Najeriya
Gangar majalisa Majalisar Taraiyar Najeriya
• Shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu (29 Mayu 2023)
Majalisar shariar ƙoli Kotun Koli Ta Najeriya
Ikonomi
Nominal GDP (en) Fassara 440,833,583,992 $ (2021)
Kuɗi Naira
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Suna ta yanar gizo .ng (en) Fassara
Tsarin lamba ta kiran tarho +234
Lambar taimakon gaggawa *#06# da 199 (en) Fassara
Lambar ƙasa NG
Wasu abun

Yanar gizo nigeria.gov.ng

Najeriya (/naˈdʒɪəriyə/) ko Nijeriya (/niˈdʒɪəriyə/) da (turanci: Nigeria), A gwamnatance Tarayyar Najeriya, ƙasa ce da ke a Afirka ta Yamma. Tana da iyaka da kasarNijar daga Arewa da Chadi daga Arewa, maso gabas da Kamaru daga gabas da Benin daga Yamma daga Kudanci kuma tana a gaɓar Tekun Atlantika. Jamhuriyar Tarayyar Najeriya, ta ƙunshi Jihohi guda 36, tare da babban birnin tarayya (Federal Capital Territory) Abuja inda fadar shugaban ƙasa take.[1][2][3]

Abuja tana daya daga cikin manyan birane a duniya.[4]

Shopping District

Najeriya ta kasance gida da dama ga 'yan asalin Turawa masu mulkin mallaka, jihohin da suka mallaka tunda (BC), tare da Nok Wayewa ta kasance ita ce karo na farko da Turawan mulkin mallaka suka fara mallakewa a Yammacin Africa a cikin ƙarni na 15 A zamani jihar an samo asali da Birtaniya a cikin ƙarni na 19, yana ɗaukar yanayin na yanzu tare da haɗe yankin Kudancin Najeriya da kuma kare Arewacin Najeriya a cikin shekara ta alif dubu daya da Dari Tara da goma sha hudu (1914) ta Lord Lugard. Ingilishi ya kafa tsarin gudanarwa da na doka yayin aiwatar da mulkin kai tsaye ta hanyar shugabannin gargajiya.[5] Najeriya, ta zama ƙasar tarayyar da ke da ƴanci kai tsaye a ranar 1 ga watan Oktoba, shekara ta alif dubu daya da dari tara da sittin (1960). Ta fuskanci yaƙin basasa daga shekara ta 1967 zuwa shekarar 1970, sannan a biyo bayan zaɓaɓɓun gwamnatocin farar hula da mulkin kama-karya na soja, har sai an sami tabbatacciyar dimokuradiyya a shekara ta alif 1999; zaɓen shugaban ƙasa na shekara ta 2015, shi ne karo na farko da shugaban ƙasa mai ci ya faɗi zaɓensa. [6][7]

Najeriya ƙasa ce mai yawan Al’umma da ke zaune, sama da ƙabilu guda Dari, biyu da hamsin (250), waɗanda ke magana da yarurruka daban daban guda 500, dukkansu suna ɗauke da al'adu iri daban daban. [8][9] [10] Manyan ƙabilun guda uku su ne Hausa – Fulani a Arewa, Yarbawa a Yamma, da kuma Igbo a gabas, waɗanda suka haɗa da kashi 60% na yawan mutanen. [11] Yaren hukuma shi ne Ingilishi, wanda aka zaɓa don sauƙaƙe haɗin harshe a matakin ƙasa. [12] Tsarin mulkin Nijeriya ya tabbatar da ƴancin yin addini ; [13] kuma ƙasa ce dake ɗauke da Al’ummar musulmai da Kirista, a lokaci guda. [14] Najeriya ta kasu kashi biyu tsakanin musulmai, waɗanda yawanci ke zaune a arewacin ƙasar, da kuma kiristoci, waɗanda yawanci ke zaune a kudancin ƙasar, tare da ƴan tsirarun da ke yin addinin asali, kamar waɗanda ke cikin ƙabilar Igbo da kuma yarbawa.[15][16][17]

Bola Tinubu shugaban kasar na yanzu

Najeriya ita ce ƙasa mafi yawan mutane a Afirka, kuma ƙasa ta bakwai mafi yawan mutane a Duniya, tare da kimanin mutane miliyan 206. Tattalin arziƙinta shine mafi girma a Afirka, kuma shi ne na 26 mafi girma a duniya ta hanyar GDP maras faɗi, kuma na 25 mafi girma daga PPP. Najeriya galibi ana kiranta da "Giant of Africa", ma'ana ƙarfin Afrika saboda yawan jama'a da tattalin arziƙinta, [18] kuma Bankin Duniya yana ɗaukarta a matsayin kasuwa mai tasowa. Ƙaramar yanki ce a cikin Afirka, matsakaiciyar ƙarfi a cikin al'amuran ƙasa da ƙasa, sannan kuma tana ɗaya daga cikin ƙasashe mafi yawan Al’umma a duniya. Koyaya, ƙasar tana ƙasa sosai a cikin jerin ƙasashen duniya, kuma har yanzu tana ɗaya daga cikin ƙasashe masu rashawa a duniya. [19] [20] Najeriya memba ce ta kafuwar Tarayyar Afirka, kuma memba ce a ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da dama, waɗanda suka haɗa da Majalisar Ɗinkin Duniya, ƙungiyar ƙasashen Yammacin Africa (ECOWAS), kungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur, (OPEC), kuma memba na yau da kullum a gamayyar MINT, kuma tana ɗaya daga cikin Ƙasashe goma sha ɗaya masu tashen ƙaruwan tattalin arziƙi wato "Next Eleven".[21]

  1. http://www.unep.org/news-and-stories/story/unep-ogoniland-oil-assessment-reveals-extent-environmental-contamination-and
  2. https://www.greenleft.org.au/content/shell%E2%80%99s-nigeria-ecocide-creating-refugee-crisis,%20https://www.greenleft.org.au/content/shell%E2%80%99s-nigeria-ecocide-creating-refugee-crisis[permanent dead link]
  3. https://web.archive.org/web/20141205124719/http://www.punchng.com/news/us-sends-medical-experts-to-study-how-nigeria-contained-ebola/
  4. Muhammadu Buhari
  5. Achebe, Nwando, 1970-. The female king of colonial Nigeria : Ahebi Ugbabe. Bloomington. ISBN 978-0-253-00507-6. OCLC 707092916.CS1 maint: multiple names: authors list (link)
  6. https://www.theguardian.com/society/2015/may/29/outlawing-fgm-nigeria-hugely-important-precedent-say-campaigners
  7. "Buhari wins historic election landslide". Reuters (in Turanci). 2015-03-31. Retrieved 2020-05-25.
  8. Empty citation (help)
  9. Empty citation (help)
  10. Empty citation (help)
  11. Empty citation (help)
  12. Empty citation (help)
  13. Empty citation (help)
  14. Empty citation (help)
  15. https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/520849-number-of-poor-people-in-nigeria-to-reach-95-million-in-2022-world-bank.html
  16. https://www.washingtonpost.com/outlook/2019/09/16/official-us-poverty-rate-is-based-hopelessly-out-of-date-metric/
  17. Empty citation (help)
  18. Empty citation (help)
  19. Empty citation (help)
  20. Empty citation (help)
  21. https://www.fao.org/nigeria/fao-in-nigeria/nigeria-at-a-glance/en/

From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Nelliwinne