Manoma | |
---|---|
sana'a | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | agricultural worker (en) , field crop and vegetable growers (en) da Q126838368 |
Field of this occupation (en) | noma da farming (en) |
Depicted by (en) | Statue of the Farmer (en) |
ISCO-88 occupation class (en) | 6111 da 9212 |
Manoma jam'in kalma ce ta manomi sannan kalmar ta samo asali ne daga Noma. Manoma suke noma dukkan kayan masarufi na abinci kamar irinsu hatsi, borkono, tarugu, tumatur, tattasai, alaiyahu, kabeji, latas da dai sauran su. Manoma sun kasu zuwa kashi biyu ne (2). Akwai masu noman rani akwai kuma masu na Damina da kuma na zamani duk da kuma dai yanzu kusan duka manoma suna amfani da kayayyakin zamani. Sai dai wani lokacin manoma suna fuskantar kalubale da matsalolin rashin kayan aiki da don saboda rashin tallafin daga gwamnati zaka hasashe ya nuna kaso kusan saba'in (70) cikin dan Najeriya manoma ne amma saboda babu cikakkun kayan aiki da tallafi shi yasa harkokin noma ba su bunkasa ba.[1]