Musulunci

Musulunci
Founded 631
Mai kafa gindi Muhammad
Classification
Sunan asali الإسلام
Practiced by Musulmi da ummah (en) Fassara
Branches Rukunnan Musulunci
Shahada
Sallah
Zakka
Azumi A Lokacin Ramadan
Aikin Hajji
Wata yarinya a Karanta Alqur'ani Mai girma
dakin Allah (S WA)
gurin ibadan musulmai

Addinin Musulunci (Islama;[1] Larabci: ٱلْإِسْلَام‎, romanized: al-Islām, Turanci: Islam) Shine shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad (S A W) bawan Allah ne kuma manzon Allah ne.

Addinin yana da alaƙa da Annabi Ibrahim kuma ya ƙunshi hukunce hukunce daga Alkur'ani da kuma koyarwar Manzon tsira wanda shine ya zo da littafin sannan akwai aƙalla mabiya addinin musulunci mutum biliyan ɗaya da ɗugo tara (1.9B). Addinin musulunci shine addini na biyu dangane da yawan mabiya bayan addinin Kirista.[2]

Annabi Muhammad (S AW) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi,[3] shine manzo wanda Allah ya aiko shi zuwa ga mutane baki ɗaya kuma na ƙarshen/cikamakin annabawa a duniya domin ya sake jaddada addinin Allah, a yi imani da Allah wanda ya halicci kowa da komai.

Addinin musulunci na da mabiya a duk faɗin ƙasashen duniya kuma mafiya yawa su na zaune ne a yankin gabas ta tsakiya, da yankin Afirka ta arewa waɗanda mafi yawancinsu Larabawa ne masu bin addinin musulunci, sai dai akwai ɗinbin mabiya addinin musulunci a ko'ina a faɗin duniya.[4] Ma'anar addinin Musulunci shine yarda da miƙa wuya da kaɗaita Allah Maɗaukakin Sarki, wato shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammad (s.a.w) Manzon Allah ne.

Musulmai sunyi imani cewa addinin Musulunci shine cikakken addini kuma addini na gaskiya wanda aka turo Annabawa da manzanni da yawa a baya, wanda suka haɗa da kakanmu Annabi Adamu, Annabi Nuhu, Annabi Ibrahim, Annabi Musa da kuma Annabi Isah.

Har wayau, Musulmai sunyi imani cewa Alƙur'ani maganar Allah ne, kuma saƙon Ubangiji ne na ƙarshe wanda babu tawaya a cikin shi. Tare da AlKur'ani, Musulmai sunyi imani da sauran littattafan da aka turo kamar Attawra, Zabura da Injila. Kuma Annabi Muhammad (SAW) shine cikamakin Annabawan Musulunci, kuma ta shine addinin Musulunci ya cika. Koyarwarsa da umurninsa ana ƙiran su da Sunnah wanda aka rubuta a littattafai da ake ƙira Hadisi, wanda ke koyar da tsarin mulki da rayuwa.

  1. "English pronunciation of Islam". Cambridge Dictionary. Archived from the original on 22 January 2021. Retrieved 19 Dec 2023.
  2. "Pew-Templeton Global Religious Futures Project - Research and data from Pew Research Center". 21 December 2022. Archived from the original on 5 February 2023. Retrieved 27 November 2023.
  3. https://dictionary.cambridge.org/pronunciation/english/islam
  4. https://www.britannica.com/topic/Islam

From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Nelliwinne